Shugaban Kasar Rasha Ya Ce Harkokin Kasuwanci Tsakanin Rasha Da Iran Suna Kara Habaka

Shugaban kasar Rasha Vladimit Putin ya bayyana cewa harkokin kasuwanci da kuma tattalin arziki tsakanin Rasha da Iran suna kara habaka, ya kuma kara da

Shugaban kasar Rasha Vladimit Putin ya bayyana cewa harkokin kasuwanci da kuma tattalin arziki tsakanin Rasha da Iran suna kara habaka, ya kuma kara da cewa kasar Iran abin dogaro ne sosai a wadanan bangarori.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto shugaba Putin yana fadar haka a jawabin da ya gabatar a yau Laraba a birnin Mosco, a kuma taron zuba jari na bankin VTB karo na 15.

Bankin VTB dais hi ne banki na biyu a girma a kasar Rasha. Shugaban ya kuma kara da cewa a halin yanzu kasar Rasha tana harkokin kasuwanci a bangarorin, makamashi, masana’antu, tsaro da wasu wurare da kasar Iran.

Shugaban ya kara  da cewa kasashen biyu suna aiki tare don habaka bangaren jigilar kayaki da tafiye-tafiye ta layin dogo. Yace: A halin yanzu layin dogon da ake kira ‘koridon Arewa da Kudu, ya fara habaka, kuma idan hakan ya ci gaba, kasashen biyu zasu amfana da shi. Shugaban ya kammala da cewa, ‘a cikin ziyarar da ake saran shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan zai kawo birnin Mosco nan gaba ne, kasashen biyu zasu rattaba hannu kan yarjeniya ta musamman ta kuma harkokin kasuwanci mai dogon zango

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments