A jiya Laraba ne dai jirgin shugaban kasar ta Iran ya sauka filin saukar jiragen sama na “John F. Kennedy” a birnin New-York domin halartar taron shekara-shekara na babban zauren MDD,inda ya sami tarbar jakadan jamhuriyar musulunci a Majalisar Gulam Hussai Durzi.
A yayin zamansa a birnin New York, shugaban kasar ta Iran zai gabatar da jawabi da aciki zai bayyana riwayar Iran akan abinda yake faruwa na kallafaffen yaki na uku akan Iran da kuma zaluncin da ake yi ma ta.
Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran zai gana da takwarorinsa na kasahsen duniya domin tattauna bunkasa alaka a tsakaninsu da kuma hanyoyin fadada ta.
Akan hanyarsa ta zuwa Amurkan, shugaban kasar ta Iran ya yada zango a kasar Aljeriya inda ya sami kyakkyawar tarba a filin saukar jiragen saman a birnin Alges.
Tawagar ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Arakchi ta fara yin gaba zuwa birnin na New-york tun a ranar Talatar da ta gabata, tare da ganawa da takwarorinsa na kasashe mabanbanta.
Taron babban zauren na MDD na wannan shekarar zai zama karo na 81 a matakin shugabannin kasashe da gwmanatoci daga kasashe 193. Taron zai ci gaba daga nan har zuwa 28 ga watan nan na Satumba.