Pezeshkian Ya Jaddada Wajabcin Haduwar Kasashen Musulmi Wajen Hana Laifukan Yaki A Gaza

Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa; Dole ne kasashen musulmi su hana ci gaba da aikata laifuka a Gaza Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin

Shugaban Kasar Iran ya jaddada cewa; Dole ne kasashen musulmi su hana ci gaba da aikata laifuka a Gaza

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian, yayin wata tattaunawa ta wayar tarho da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim, ya jaddada bukatar kasashen musulmi su dauki matakin hana ci gaba da bala’in jin kai a Gaza ta hanyar diflomasiyya da kuma matsin lamba na siyasa.

A safiyar yau Laraba ne shugaba Pezeshkian ya tattauna da fira ministan Malaysia Anwar Ibrahim ta wayar tarho, inda ya jaddada cewa: “Aikin ta’addancin da gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta aiwatar a Gaza ba abin da za a amince da shi ba ne ga kowane mai ‘yanci,” yana mai bayyana fatansa na ganin “kasashen Musulmi za su yi aiki tare da hadin kai, ta hanyar diplomasiyya mai inganci, don hana ci gaba da wadannan laifuka.”

Pezeshkian ya kuma kara da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta kasance mai kare hakkin al’ummar Falastinu da ake zalunta, inda ta yi kira ga sauran kasashen musulmi da su kara daukar matakai masu tsauri da tasiri wajen nuna goyon baya ga Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments