Shugaban Kasar Iran Ya Jaddada Aniyarsu Ta Daukan Fansar Kisan Gillar Haniyah

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Za su sanya gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi nadama kan matakin da ta ɗauka na aiwar da kisan gilla

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Za su sanya gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta yi nadama kan matakin da ta ɗauka na aiwar da kisan gilla kan Isma’il Haniyah

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya fitar da sanarwar mayar da martani kan kisan gillar da aka yi wa Isma’il Haniyeh shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas na Falasdinu a birnin Tehran fadar mulkin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Pezeshkian ya ce: A yau Iran na zaman makoki da bakin ciki rashin abokinta na har abada a kan turbar gwagwarmaya, jajirtacce kuma jagoran gwagwarmayar Falastinawa kuma shahidin Qudus Isma’il Haniyyah, sannan Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta sanya ‘yan ta’adda yahudawan sahayoniyya kuma ‘yan mamaya su yi nadamar kisan gillar da suka yi wa jarumin shahidan Qudus Haj Isma’il Haniyeh a jiya, wanda ya daga hannun shugaban Iran a Majalisar Shawara Musulunci saboda samun nasarar da ya yi na dare karagar shugabancin Iran, Pezeshkian yana jaddada cewa; A yau dole ne ya dauke shi a kafadarsa zuwa jana’izarsa.

Yana mai jaddada cewa: Dangantaka tsakanin al’ummar Iran da na Falasdinu za ta yi karfi fiye da kowane lokaci, kuma Iran zata ci gaba da goyon bayan tafarkin gwagwarmaya fiye da kowane lokaci, kamar yadda zata sanya ‘yan ta’addan yahudawa yin nadamar ayyukan ta’addanci da suka aikata na tsoro da ragwanci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments