Shugaban Kasar Iran Ya Fadawa Muhammad Bin Salman Kan Cewa Tehran Tana Shirin Kare Kanta

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a zantawarsa tan wayar tarho da yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya sannan Firai ministan kasar Muhammad bin Salman

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkiyan a zantawarsa tan wayar tarho da yerima mai jiran gadon sarautar kasar Saudiya sannan Firai ministan kasar Muhammad bin Salman ya taya shi murnin salla karama ya kuma yiawa dukkan kasashen musulmi fatan alkhairi.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban yana cewa, JMI bata neman yaki da kowa amma kuma a shirye take ta kare kanta a duk lokacinda wani ya takaleta.

Pezeshkiyan ya kara jaddada cewa shirin Nukliyar kasar Iran ta zaman lafiya ne, kuma wannan kamar ydda hukumar makamashin nukliya ta duniya IAEA ta tabbatar. Banda haka kamar yadda yake a shekarum baya, hukumar zata ci gaba da bincike don tabbatar da hakan.

A wani bangare na maganarsa shugaban yayi kira ga kasashen musulmi su hada kai, saboda warware matsalolin da kasashen yankin suke fuskanta daga ciki da na al-ummar Falasdinu. Ya ce yana da kekyawar zato kan cewa kasashen musulmi a yankin su kai suna iya kula da zaman lafiya a yankin ba tare da shigar wasu kasashen waje ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments