Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana ci gaba da aiwatar da mummunan kisan gilla kan al’ummar Falasdinu a yankin Zirin Gaza da sunan kare kai.
Wannan dai ya zo ne a cikin wata sanarwa da shugaba Pezeshkian ya fitar, a jiya Laraba, a gaban wani taron ginin cibiyar shawarwarin al’adun Iran a birnin Bagadaza fadar mulkin kasar Iraki a gaban gungun ‘yan kasar Iran mazauna Iraki.
Shugaban ya kara da cewa: Idan wani karamin lamari ya faru a kasar Iran, kafafen yada labaran duniya su kan yi gaggawar yada labarin da kuma yada “taken neman kare hakkin dan Adam a Jamhuriyar Musulunci”. To sai dai kuma ana ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi kan mutane masu dimbin yawa sakamakon hare-haren bama-bamai da makamai masu linzami da yahudawan sahayoniyya suke kai wa kan mata da kananan yara da matasan Falasdinawa gami da tsofaffi, to amma duniyar da ke da’awar kare hakkin bil’adama ta yi shiru kan dukkanin wadannan laifuka.
Shugaban na Iran ya ci gaba da cewa: Kasashen duniya sun kasa kawo karshen wannan kisan kiyashi, kuma suna ganin hakan tamkar kare kai ne. Ya bayyana wannan tsari da duniyar yammaci ke bi a yau game da abubuwan da ke faruwa a Gaza, a matsayin “kisan yanke tsammani ga matasa masu tasowa.”