Shugaban Iran Ya Ce Gudanar Da Kyakkyawan Tsari Zai Mayar Da Iran Tushen Samar Da Iskar Gas

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Gudanar da kyakkyawan tsari zai mayar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa tushen samar da iskar gas a yankin

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Gudanar da kyakkyawan tsari zai mayar da Jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa tushen samar da iskar gas a yankin Gabashin Asiya

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kasashen Iran da Turkmenistan a fannin iskar gas, wani kyakkyawan mataki ne mai ma’ana da zai mayar da Iran zuwa wata tushen samar da iskar gas da zata amfanar tare da zama babban abin Moriya ga kasashen biyu.

A zaman taron hadin gwiwa na manyan tawagogin kasashen Iran da Turkmenistan a jiya Laraba, shugaba Pezeshkian ya kara da cewa: Shi da kansa zai bi diddigin yarjejeniyoyin da aka kulla tsakanin kasashen biyu da kuma alkawurran da aka dauka a tsakaninsu.

Shugaban ya kuma jaddada cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta himmatu wajen tabbatar da yarjejeniyoyin da aka kulla tsakaninta kasar Turkmenistan, kuma a shirye take ta shawo kan matsalolin da ke kawo cikas wajen aiwatar da su da kuma fadada dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments