Shugaban Kasar Iran Ya Bude Wata Madatsar Ruwa Wanda Iran Ta Gina A Sirilanka

Shugaan kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta bawa kasar Sirilanta fasaha da ci gaban da ta samu a

Shugaan kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa kasarsa a shirye take ta bawa kasar Sirilanta fasaha da ci gaban da ta samu a bangarorin ilmi daban daban.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ra’isi yana fadar haka a a ziyarar da yakr yi a kasar Sirilanka inda ya bude wata madatsar ruwa wanda Omouyo wacce masana iraniyawa suka gina.

Ya kuma kara da cewa kasar Iran shirye take ta yi musaya da kasashen Asia irin ci gaban da take samu a bangarorin ilmin fasaha da ci gaban ilmi.

Ya ce kasashen yamma suna ganin su kadai yakamata su ci gaba a duniya, don haka suke hana sauran kasashen duniya ci gaban da yakamata su samu.

Ya kuma kara jaddada cewa kasashen Asia suna da makoma mai kyau nan gaba a bangaren ci gaban ilmi da fasaha.

Daga karshe ya kamala da cewa irin ci gaban da kasar Iran take samu gogewa ne na shekaru kimani 45 da suka gabata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments