Jaridar “Jerrusalem Post” wacce ake bugawa a HKI ta yau Lahadi ta yi ishara da wata wasika ta babban hafsan hafsoshin sojan HKI Herzi Halevi da a ciki yake yin furuci da cewa sun ci kasa a hannun ‘yan gwgawarmayar Falasdinawa.
Jaridar ta kuma bayyana cewa anan gaba za a rika tuna babban hafsan hafsoshin sojan kasar ta HKi a matsayin wanda sojoji su ka sami koma bayan da cin kasar da ba su taba ganin irinsa ba.
A halin da ake ciki a wannan da akwai kwamandojin sojan HKI da dama wadanda suke gabatar da takardun na barin aiki saboda shan kasar da su ka yi sanadiyyar farmakin “ Guguwar Aqsa” da abubuwan da su ka biyo baya.
A yau Lahadi ne dai majalisar sojan HKI ta yi zama domin tattauna wasikun da kwamandoji suke gabatarwa na ajiye aikinsu saboda shan kashi a yakin Gaza.
Daga cikin wadanda su ka ajiye aikin nasu da akwai Aharun Haliva wanda ya kasance shugaban rundunar leke ta soja, sai kuma shugaban kungiyar leken asiri ta cikin gida Shabak Ronin Bar.