Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan kare hakkin bil’adama a yankin Falasdinu, Francesca Albanese, ta yi nuni da cewa, dole ne a bar Dr. Abu Sitta ya ba da shaida game da kisan kiyashin da Isra’ila ke yi a zirin Gaza.
A ranar Lahadin da ta gabata, jami’ar Majalisar Dinkin Duniya ta musamman kan kare hakkin bil’adama a yankunan Falasdinu, Francesca Albanese, ta yi kira ga Jamus da ta janye matakin da ta dauka dangane da dokar hana tafiye-tafiye kan Likitan Falasdinu Ghassan Abu Sitta.
Albanese ta rubuta a shafinta na dandalin sada zumunta na X cewa: A matsayina na ‘yar nahiyar turai ina neman afuwar Dr. Abu Sitta kan matakin da Jamus ta dauka, wanda yake nuni da wani sabon mataki na kare kisan kare dangi da “Isra’ila” ta yi daga bangaren mahukuntan Jamus, wanda Abu Sitta ya kasance mai shaida kai tsaye dangane da laifukan yaki da Isra’ila take tafkawa.
Ta nuna a cikin sakonta cewa “Dole ne a bar Dakta Abu Sitta ya ba da shaidarsa, kuma dole ne a karbe shi da girmamawa wanda ya cancanci hakan.”
Tun da farko dai Jamus ta yanke shawarar dakatar da Dakta Abu Sitta shiga dukkan yankunan kasarta na tsawon shekara guda.
A nata bangaren, mai magana da yawun jam’iyyar NPA ta Faransa Pauline Salange, ta shaida wa Al-Mayadeen cewa, “Shugabannin Turai suna yin munafunci yayin da suke yakar duk wanda baya goyon bayan laifukan Isra’ila, kuma Faransa na ci gaba da tallafa wa Isra’ila ta fuskacin ayyukan soja.”
Ta kara da cewa hana Dr. Ghassan Abu sitta zuwa kotu domin bada shaida, na da nufin boye bayanai kai tsaye daga gwamnatin Faransa kan laifukan yaki da kisan kiyashin Isra’ila a Gaza.