Search
Close this search box.

Hamas : Ba Zamu Amince Da Duk Wata Yarjejeniyar Da Ba Zata Kawo Karshen Yaki Ba

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ba za ta amince da yarjejeniyar sulhun da ba ta kawo karshen kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta ce ba za ta amince da yarjejeniyar sulhun da ba ta kawo karshen kisan kare dangi da gwamnatin Isra’ila ta kwashe kusan watanni bakwai tana yi a zirin Gaza ba.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya rawaito wani babban jami’in kungiyar da ya nemi a sakaya sunansa , yana cewa ba batun amincewa da waata yarjejeniyar sulhu idan Isra’ila ba ta dakatar da yakin da take yi ba.

Akalla Falasdinawa 34,654 ne suka rasa rayukansu a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, lokacin da gwamnatin Isra’ila ta fara fara maida martani ga harin ba zata da kungiyar Hamas ta kai mata.

Jami’in ya ce gwamnatin kasar na kokarin cimma yarjejeniyar da za ta ba da damar sako wadanda aka kama a lokacin harin “ba tare da alakanta ta da kawo karshen hare-haren da ake kaiwa Gaza ba.”

Jami’in ya kasar da cewa  dagewar da firaministan Isra’ila ya yi na kai farmaki ta kasa kan birnin Rafah da ke kudancin Gaza, wani babban cikas ne a tattaunawar da ake yi da nufin cimma yarjejeniya.

Share

1 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments