Shugaban kasar Azerbaijan Ilham Aliev ya jinjnawa shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan saboda goyon bayan kasarsa ta zama Memba a cikin kungiyar kasashen musulmi masu tasowa ta D-8.
A wata wasika da ya aiko wa shugaban kasar ta Iran, shugaba Ilham Aliev ya yaba wa kokarin kasar Iran na ganin kasarsa ta zama daya daga cikin mambobin kungiyar D-8 wacce ta kasashen musulmi masu tasowa ce.
Shugaba Aliev ya kara da cewa yadda Iran din ta goyi bayan kasarsa ya nuna yadda karfin kawance a tsakaninsu yake hakaba , haka nan kuma alaka mai karfi a tsakaninsu da kuma sauran mambobin kungiyar ta kasashen musulmi masu tasowa.
Shugaban kasar ta Azerbaijan ya kuma ce kasarsa tare da sauran kasashen kungiyar za su taka rawa wajen ganin an habaka muhimman ginshikan da aka gina kungiyar a kansu.
Haka nan kuma ya yi fatan ganin cewa kawance a tsakanin kasar tasa da Iran wacce makwabciyarta ce ya cigaba da bunkasa ta yadda dukkanin kasashen biyu da al’ummunsu za su amfana.
Ita dai kungiyar D-8 ta kasashen musulmi masu tasowa an kafa ta ne a 1997 domin habaka cinikayya a tsakaninsu, ta kuma kunshi Ira, Turkiya, Masar, Nigeria, Pakistan, Indonesia, Malyasia da kuma Bangaladesh.