Shugaban Kasar Amurka Ya Lissafa Laifukan Yakin Da Yake Son Aikatawa Akan Iran A Gaban MDD

Shugaban Kasar Amurka Ya Lissafa Laifukan Yakin Da Yake Son Aikatawa Akan Iran A Gaban MDD
shugaban kasar Amurka

Shugaba Donald Trump na Amurka wanda ya gabatar da jawabi a MDD a jiya Talata ya bayyana cewa; Zai rusa Iran, idan ba a kulla yarjejeniya da ita ba.

Jawabin na shugaban kasar ta Amurka ya kasance cike da barazana da ya kunshi cewa: Shi ne wanda ya fuskanci barazana da kalubale da wasu shugabannin su ka kau da kai daga gare su.”

Haka nan kuma ya ce; Da akwai muhimman matakai da suke a gabansa da yake son dauka,ko dai a yi yarjejeniya ko kuma in rushe kasar a cikin sauri da gaggawa da jefa ta cikin jahannama ba tare da bayar da damr rayuwa gare ta ba.”

Wannan dai zai iya zama karo na farko da wani shugaban kasa ya tsaya a gaban Majalisar Duniya da nan ne cibiyar kare dokokin kasa da kasa, yana yin baraza da bugun kirji akan laifukan yakin da yake son aikatawa a duniya.

Bugu da kari, shugaban kasar ta Amurka ya yi barazanar kakaba wa kotun duniya ta manyan laifuka takunkumai.

Jawabin na shugaban kasar Amurka dai yana zuwa ne a daidai lokacin da farinjinsa ya fadi kasa warwaa zuwa 3%, saboda tabarbarewar tattalin arzikin kasar. Farashin Galon na man fetur a cikin wasu jahohin yana a tsakanin Dala 8 zuwa 10 a wasu jahohin.

A cikin watan Nuwamba na wannan shekarar ne dai za a yi zabukan tsakiya na ‘yan majalisa da zai iya sa jam’iyyar “Republican” mai Mulki ta sami koma baya, lamarin da zai iya kai wa ga tsige Donald Trump daga kujerar Mulki idan har jam’iyyar “Democrat” ta sami rinjaye mai yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted