Shugaban Kasar Amurka Ya Janye Daga Takarar Shugabanbcin Kasar A Zabe Mai Zuwa

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yanke shawarar janyewa daga takarar shugabancin kasa a jam’iyyarsa ta Democrate ya kuma ce zai maida hankalinsa ga ayyukan

Shugaban kasar Amurka Joe Biden ya yanke shawarar janyewa daga takarar shugabancin kasa a jam’iyyarsa ta Democrate ya kuma ce zai maida hankalinsa ga ayyukan da suka rage masa a matsayin shugaban kasa na yan watanni da suka rage masa.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Biden yana fadar haka a shafinsa na X ya kuma kara da cewa yana goyon bayan mataimakiyarsa Kamal Haris a matsayin yar takara a taron da jam’iyyar zata gudanar nan gaba don zaben wanda zai maye gurbinsa.

Janyewar shugaban dai ya sanya jikin yan jam’iyyar yayi sanyi, saboda ganin saura watanni 4 kacal a je zaben shugaban kasa a kasar, suna ganin kafin a yi zabe sabon dan takara sannan a sake shiga yakin neman zaben wanda zai kara da Trump na Jam’iyyar Republican, lokaci yana iya kure masu.

Banda Kamal Haris mataimakin shugaba  kasa dai, akwai Pete Buttigieg wanda ya taba shiga takarar neman a zabe shi a matsayin dan takara, haka ma gwamnan jihar  Calfonia da suaransu na daga cikin wadanda mai yuwa zasu shiga takarar zama dan takarar jam’iyyar. Biden dai yana da matsalar mantuwa da kuma tsufa da suke rikita shi a wasu lokuta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments