Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da kafa gwamnatin hadin kan kasa da ta kunshi ‘yan adawa tare da jam’iyyarsa ta National Congress Party.
Ramaphosa ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar tahanyar kafar talabijin din kasar a yammacin ranar Lahadi, inda ya bai wa jam’iyyun adawa a sabuwar gwamnatin hadin kan kasar kujerun ma’aikatu 12 daga cikin 32, yayin da jam’iyyarsa ta National Congress Party ta samu kujeru 22 da suka hada da manyan mukamai kamar na kudi, harkokin waje. makamashi da tsaro.
A karkashin tsarin sabon kawancen, jam’iyyar Democratic Alliance – babbar jam’iyyar adawa – ta sami mukaman ministoci 6, da suka hada da ilimi, ayyukan jama’a da muhalli, yayin da wasu ma’aikatun 6 suka tafi ga kananan jam’iyyun adawa.
An nada shugaban jam’iyyar Democratic Alliance, John Steenhuisen, ministan noma a gwamnatin da aka kafa bayan shafe makonni ana tattaunawa.
Ya zama dole ga jam’iyyar National Congress Party mai Mulki a kasar, kafa gwamnatin hadin kan kasa bayan da ta rasa rinjaye a majalisar dokokin kasar a karon farko cikin shekaru 30 a zaben da aka gudanar a ranar 29 ga watan Mayun wannan shekara.