Shugaban Kasa Da Ministocinsa Sun Jaddada Bai’a Ga Wanda Ya Kafa JMI A Safiyar Yau Asabar A nan Iran

Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar

Shugaban kasar Iran Ma’suod Pezeskiyan tare da majalisar ministocinsa sun sabonda bai’a da jagoran juyin juya halin musulunci, wanda ya kai kasar ga samun nasarar tumbuke gwamnatin sarki Muhamma Reza Sha sannan ya sannan ya kaisu ga nasarar kafa JM a Iran,  shekaru 46 da suka gabata.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a safiyar yau Asabar ce shugaban kasar Iran, Masuod Pezeshikyan tare da majalisar ministocinsa suka kara sabonta bai’a wato marigayi Immam Khomani (q).  

Labarin ya kara da cewa Sayyid Hassan Khomani, jikan Imam(q) wanda kuma yake kula da hubbaren nasa ne, ya tarbi shugaban kasar ya kuma jagorance su zuwa hubbaren kakansa Imam Khumaini(q).

Imam Khomani (q) ne ya jagoranci mutanen kasar Iran zuwa kifar da gwamnatin sarki sha, shekaru 46 da suka gabata, a ranar 11 ga watan Fabrayrun shekara ta 1979.

Wannan dai yana daga cikin Jerin shirye-shiyen da aka tsara na bukukuwan cika shekaru 46 da nasarar juyin juya halin musulunci a kasar Iran. Wanda za’a kamala shi a ranar 22 ga watan Bahman na shekara ta 1403.

Ana fara bukukuwan cika shekaru 46 da nasarrar juyin juya halin musulunci a kasar Iran ne tun ranar 1 ga watan Farairu 2025 a duk fadin kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments