Shugaban Jam’iyyar Adawa A Burtaniya Ya Ce HKI Tana Yaki A Gaza Ne A Madadin Gwamnatin Kasar

Shugaban wata jam’iyyar adawa a kasar Burtaniya ya bayyana cewa HKI tana yakar Falasdinawa a Gaza ne a madadin gwamnatin kasar tunda har yanzun gwamnatin

Shugaban wata jam’iyyar adawa a kasar Burtaniya ya bayyana cewa HKI tana yakar Falasdinawa a Gaza ne a madadin gwamnatin kasar tunda har yanzun gwamnatin kasar Burtaniya tana ganin gwamnatin HKI tana kare kanta daga mayakan Hamas, kuma bata daukar abinda HKI take yi a Gaza, kissan kiyashi ne.

Badenoch shugaban jam’iyyar ‘ Conservative’ ya bayyana haka ne a lokacinda yake hira da tashar talabijin ta Sky News dake birnin London a jiya Lahadi.

A lokacinda aka tambaye shi idan ya yarda da maganar Banyamin natanyaho kan cewa hamas yan ta’adda ce, kuma yana kokarin kwace gaza da shafi yan ta’adda ne, sai shugaban Conservative ya ce banzo nan don binciken kalmomin Natanyahu ba. Abinda nake son bada sanarwansa shi ne HKI tana yaki ne a madadin gwamnatin kasar Burtaniya, kamar yadda kasar Ukraine take yakar kasar Rasha a madadin kasashen turai.

Banda haka gwamnatin ta ki ta aibata HKI sannan bata yarda cewa cewa tana aikata kissan kiyashe ne a gaza ba.

Shugaban conservative yana fadar haka ne bayanda shugabannin kasashen Faransa, Burtaniya da kuma Canada suka bukaci HKI ta dakatar da kissan kiyashi na gaza ta kuma bar kayakin agaji su shiga yankin idan ba haka ba suna iya daukar matakai masu tsauri a kanta. Badenoch  Shugaban jam’iyyar Conservative ya ce wannan bai wadatar ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments