Shugaban Iran Ya Jaddada Yin Koyi Da koyarwar Imam Husaini {a.s} Domin Zama Mutane Na Kirki

Zababben shugaban kasar Iran ya jaddada aniyarsa ta tafiya a kan tafarkin gaskiya da adalci a matsayin koyi da Imam Husaini (a.s) Zababben shugaban kasar

Zababben shugaban kasar Iran ya jaddada aniyarsa ta tafiya a kan tafarkin gaskiya da adalci a matsayin koyi da Imam Husaini (a.s)

Zababben shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya bayyana cewa: Tafarkin Imam Husaini (a.s) shi ne tafarkin gaskiya da adalci, idan kuma ba mu bi tafarkin adalci ba, to abin da za mu yi wa Imam Husaini (a.s), kuka ne kawai ba wani abu ba.

A jawabin da ya gabatar a yammacin ranar Litinin da ya gabata a jajibirin Ashura a hubbaren Imam Khumaini (r.a) da ke birnin Rey da ke kudancin birnin Tehran fadar mulkin kasar, Pazshkian ya ce: Muna da ka’ida na tushe mai sunan gaskiya da adalci, kuma Imam Husaini (a.s) ya zo ne domin tabbatar da gaskiya da adalci, don haka idan ba mu tabbatar da gaskiya a tsakanin al’ummomi da kabilu ba, abin da muke yi saboda Husaini (a.s) ) kuka ne kawai ba wani abu ba.

Zababben shugaban ya jaddada cewa: Idan shugabannin da jami’ai ba su yi aiki a kan tubalin adalci ba, shin mutane za su gwada bacin ransu da kuma gabatar da kokensu gare mu?

Ya ci gaba da cewa: Wannan matsayi ba wai don nunawa jama’a ba ne a matsayin alfahari, a’a sai dai don neman yi wa al’umma hidima, sannan ya kara da cewa: Wajibi ne shugabanni su yi riko da adalci, kuma kada su raba kansu da hanyar adalci da daidaito tsakanin al’umma, wannan shi ne abin da Imam Husaini (amincin Allah ya tabbata a gare shi) ya zo ya wanzar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments