Shugaban Colombia Ya Yi Kira Ga Kotun ICC Da Ta Bada Sammacin Kama Netanyahu

Shugaban Colombia ya yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ta bayar da sammacin kame firaministan Isra’ila kan kisan kiyashi

Shugaban Colombia ya yi kira ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ta bayar da sammacin kame firaministan Isra’ila kan kisan kiyashi a zirin Gaza.

Gustavo Petro ya fada a cikin wani sako na ‘’X’’ a ranar Juma’a cewa Benjamin Netanyahu ba zai dakatar da kisan gillar da ake yi ba kuma wannan yana nuna bukatar sammacin kamawa.

Shugaban na Colombia ya kuma yi kira ga kwamitin sulhu na MDD da ya kafa rundunar kiyaye zaman lafiya a zirin Gaza.

A makon da ya gabata, Petro ya sanar da cewa kasarsa ta yanke huldar diflomasiyya da Isra’ila saboda hare-haren da gwamnatin kasar ke kaiwa Gaza.

Kasashen Bolivia, Belize da Afirka ta Kudu su ma sun yanke ko kuma sun dakatar da hulda da Isra’ila.

Farmakin Isra’ila ya kori kusan kashi 80% na al’ummar Gaza miliyan 2.3 daga gidajensu, ya haifar da barna mai yawa a garuruwa da birane da dama tare da lakume rayukan mutane sama da 34,943 a fadin yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments