Jaridar Wall Street Journal ta Amurka ta rawaito cewa Hadaddiyar Daular Larabawa ta hana Amurka kai hare-hare a Yemen da Iraki ta sansanin sojin saman Al-Dhafra da ke Abu Dhabi.
Jaridar ta nakalto wani jami’in kasar yana cewa kasarsa na daukar mataki na kalubalantar hare-hare da Amurka ke kai wa a Iraki da Yemen.
Jami’in masarautar da ya bukaci a sakaya sunansa, ya jaddada cewa an dauki wannan matakin ne domin kare kai.
Jami’in ya ce an hana hare-haren da sojojin Amurka da ke sansanin Al-Dhafra suka kai wa Iraki da Yemen, saboda yadda Amurka ta yi jinkiri wajen daukar matakan kare Hadaddiyar Daular Larabawa bayan hare-haren ‘yan bindiga a kasar a farkon shekara ta 2022.