Kasuwanci Tsakanin Iran Da Tarayyar Turai Ya Karu Da Kashi 30%

Kasuwancin da ke tsakanin Iran da Tarayyar Turai ya karu da kashi 30 cikin 100 a cikin wata na biyu na wannan shekara. Kayayyakin da

Kasuwancin da ke tsakanin Iran da Tarayyar Turai ya karu da kashi 30 cikin 100 a cikin wata na biyu na wannan shekara.

Kayayyakin da Jamus ke fitarwa zuwa Iran sun karu da kashi 46 cikin 100 sannan kayayyakin da Italiya ke shigowa da su daga Iran sun karu da kashi 96.

Alkaluman baya-bayan nan da cibiyar kididdiga ta Turai (Eurostat) ta fitar na nuni da cewa ciniki tsakanin Iran da kasashe 27 na Tarayyar Turai ya kai Yuro miliyan 847 a watanni biyun farkon wannan shekara.

Kasuwancin da ke tsakanin Iran da Tarayyar Turai ya karu da kashi 8% a cikin watanni biyu na farkon shekarar 2024 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

A cikin watannin Janairu da Fabrairu na shekarar da ta gabata an yi musayar kayayyaki da suka kai Euro miliyan 780 tsakanin bangarorin biyu.

A cewar wannan rahoto, kayayyakin da EU ta shigo da su daga Iran a watanni biyun farko na shekarar 2024 sun karu da kashi 3% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata kuma sun kai Yuro miliyan 144.

A cikin watannin Janairu da Fabrairu na shekarar da ta gabata, kasashen Turai sun shigo da kayayyaki da darajarsu ta kai Euro miliyan 139 daga Iran.

Kayayyakin da EU ke fitarwa zuwa Iran a watan Janairu da Fabrairu na wannan shekara shi ma ya karu da kashi 9% idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata kuma ya kai Yuro miliyan 703.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments