Shugaban Brazil Ya Yabawa Spain Kan Hana Amfani Da Kasarta Wajen Yakar Iran

Shugaban kasar Brazil ya yaba wa Spain kan hana amfani da yankinta wajen kai hari kan Iran Shugaban Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya

Shugaban kasar Brazil ya yaba wa Spain kan hana amfani da yankinta wajen kai hari kan Iran

Shugaban Brazil Luiz Inácio Lula da Silva ya yaba da matsayin Spain na hana Amurka amfani da yankinta don kai hari kan Iran.

“َShugaban Brazil yana cewa; Yana son ya yaba…wa (Fira Minista) Pedro Sánchez kuma ya jinjiawa jarumtarsa,” in ji Lula da Silva a lokacin ziyararsa zuwa Spain a ranar Asabar.

“Bai bar jiragen saman Amurka su tashi daga Spain don kai hari kan Iran ba,”.

Brazil da Spain sun yi kira da a dakatar da fada a Gabas ta Tsakiya da kuma neman hanyoyin sulhu ta hanyar tattaunawa.

Ya kamata a lura cewa: Matsayin Spain kan hana sojojin Amurka amfani da yankin Spain da sansanonin sojinta don gudanar da ayyukan soji a kan Iran ya haifar da rikici tsakanin gwamnatin Spain da gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya yi kakkausar suka kan kin taimakon sojojin Amurka da Spain ta yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted