Shugaban kasar Argentina Javier Milei ya bukaci firaminista Benjamin Netanyahu da ya dage ziyarar da ya shirya kaiwa zuwa kasar Argentina gabanin zaben ‘yan majalisar dokokin kasar, saboda hakan na iya kara cutar da farin jininsa da tuni ya ragu.
A cewar jaridar Yedioth Ahronoth ta Isra’ila, Netanyahu ya kasance yana shirye-shiryen tafiya zuwa Buenos Aires, amma Milei ya nemi ya jinkirta tafiyar.
Da cewa da cewa Milei sananne ne wajen nuna goyon bayan ido rufe ga “Isra’ila”, an ba da rahoton cewa shugaban na Argentina ya damu da cewa ziyarar Netanyahu za ta yi masa mummunar tasiri a siyasance.
Kasar Argentina dai na daga cikin kasashen da har yanzu suke da damar karbar Netanyahu, wanda kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ke nema ruwa a jallo bisa laifin aikata laifukan yaki a Falasdinu.
An zabi Milei, dan siyasa mai ra’ayin rikau, a matsayin shugaban kasa a shekarar 2023 bayan ya lashe kashi 55% na kuri’un da aka kada. Duk da haka tun daga lokacin farin jininsa ya fuskanci koma baya sakamakon kalubale na cikin gida.
A watan Agusta, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa lauyoyin kare hakkin dan Adam na Argentina sun shigar da kara a gaban kotun tarayya suna neman a kama Netanyahu idan ya shiga kasar.
Karar dai zargin shi da hannu wajen aikata laifin yaki da ya yi sanadiyar mutuwar mutane da gangan ta hanyar saka su a cikin yunwa, da kuma laifukan cin zarafin bil’adama da suka hada da kisan kai, da kuma wasu ayyukan da ba su dace a kan dan dan adam ba.