Shugaban Amurka Ya Rattaba Hannu Kan Dokar Tura Bakin Haure Na Kasarsa Zuwa Guantanamo

Shugaban kasar Amurka ya rattaba hannu kan dokar ba da damar tsare bakin haure kusan 30,000 a sansanin Amurka da ke tsibirin Guantanamo Shugaban kasar

Shugaban kasar Amurka ya rattaba hannu kan dokar ba da damar tsare bakin haure kusan 30,000 a sansanin Amurka da ke tsibirin Guantanamo

Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya ce yana son gidan kurkukun sojoji da ke Guantanamo Bay, wanda aka kebance domin tsare fursunonin da ake zargi da ta’addanci, ya kasance a shirye domin karban bakin haure kusan 30,000 da suka shiga cikin Amurka ba bisa ka’ida ba.

Trump yana cewa: “A yau zai rattaba hannu kan wani umarni na zartarwa wanda ke umurtar ma’aikatar tsaro da tsaron cikin gida da su shirya wata cibiya da za ta karbi bakin haure 30,000 a tsibirin Guantanamo Bay,” Trump ya kara da cewa: Guantanamo zai karbi “masu aikata laifuka” a cikin wani yanayi na yau da kullun ba na sojojin yaki ba.

Shugaban na Amurka ya kuma rattaba hannu kan dokarsa ta farko tun bayan hawansa mulki a ranar 20 ga watan Janairu, wani mataki na nuna adawa da shige da fice wanda ke ba da damar tsare mutane kai tsaye a cikin wani yanayi da ba na soji ba idan aka tuhume su ko kuma aka yi musu shari’a a kan aikata wasu laifuffuka ko keta hurumin wasu dokoki.

An bude gidan yarin na Guantanamo ne a shekara ta 2002, a cikin wani sansanin sojin Amurka da ke Cuba, a matsayin wani bangare na yaki da ta’addanci da tsohon shugaban Amurka George W. Bush ya ayyana bayan kai harin ranar 11 ga watan Satumban shekara ta 2001.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments