Shugaban Amurka Ya Ce An Cimma Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta Tsakanin Pakistan Da Indiya

Shugaban kasar Amurka ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Indiya da

Shugaban kasar Amurka ya sanar da cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta tsakanin Indiya da Pakistan

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Indiya da Pakistan sun cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta nan take, wanda Amurka ta shiga tsakani wajen kulla ta.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana farin cikinsa da wannan ci gaba, da aka samu, inda ya yaba da amfani da hankali da basirar da kasashen biyu suka nuna wajen daukar wannan mataki. Ya kuma jaddada cewa, dogon tattaunawar da aka yi tsakanin bangarorin biyu ya haifar da wannan yarjejeniya, wanda ke nuna muradin bangarorin biyu na samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Wannan sanarwar ta zo ne a wani lokaci mai muhimmanci, yayin da alakar Indiya da Pakistan ke samun tangarda da kuma bullar takun-saka a tsakaninsu a ‘yan shekarun nan, musamman kan batun Kashmir.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments