Pizishkiyan:  Goyon Bayan Al’ummar Iran Ga Tsarin Musulunci Ne Ya Hana Abokan Gaba Cimma Manufa

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ne ya bayyana cewa; Yadda al’ummar Iran suke goyon bayan tsarin musulunci shi ne abinda ya          hana abokan gaba cimma

Shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ne ya bayyana cewa; Yadda al’ummar Iran suke goyon bayan tsarin musulunci shi ne abinda ya          hana abokan gaba cimma mummunar manufarsu akan kasar.

Shugaban na kasar Iran wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron girmama ranar “Mutane Masu Bukata Ta Musamman” ta duniya ya bayyana cewa a yayin kallafaffen yaki na shekaru takwas tsakanin 1980-1988, dukkanin duniya ta kasance a bayan ‘yan Ba’asiyya da zummar kawo karshen jamhuriyar musulunci,amma goyon bayan da al’ummar Iran suke bai wa tsarin musulunci ya sa hakan ba ta faru ba.

Haka nan kuma shugaban kasar ta Iran ya ce; “Yan Sahayoniya da Amurka sun kawo wa Iran hari da yakin kwanaki 12 a karkashin wannan irin tunanin na kawo karshen tsarin musulunci a cikin kwakani kadan, su kuma ingiza al’ummar kasar zuwa kan tituna su yi wat sarin musulunci bore, said ai yadda al’ummar ta Iran ta yi tsayin daka ta kare kasa da tsarin dake tafiyar da kasar, ya rusa wannan makarmashiyar ta su.

Wani sashe na jawabin shugaban kasar ya kunshi cewa wajibi ne ga gwamnati ta kasance a tare da al’ummar kasa domin warware matsalolin da suke fuskanta da kuma kare mutuncin kasa da ‘yancinta.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments