Pezeshkian Ya Jaddada Muhimmancin Hadin Kai A Tsakanin Kasashen Yankin Domin Fuskantar HKI

Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian Ya Jaddada Muhimmancin Hadin Kai A Tsakanin Kasashen Yankin Domin Fuskantar HKI ya yi ishara da kisan kiyashin da HKI

Shugaban kasar Iran Mas’ud Pezeshkian Ya Jaddada Muhimmancin Hadin Kai A Tsakanin Kasashen Yankin Domin Fuskantar HKI ya yi ishara da kisan kiyashin da HKI take yi a cikin kasashen yankin, sannan ya kara da cewa: Idan har za mu hada kai,to wannan haramtacciyar kasar ba za ta iya cigaba da aikata laifukan da take yi ba a cikin wannan yankin.

A hirar da tashar talbijin din “Aljazira” ta yi da shi, shugaban kasar ta Iran ya ce; Abin takaici ne a ce Amurka da kasashen turai suna kare laifukan da HKI take aikatawa.

Shugaban ya kara da cewa; HKI ba ta cimma manufofin da ta sa a gaba ba a cikin wannan yankin , kuma ba ta yi galaba akan kungiyoyin gwgawarmayar Falasdinu ba.”

Danagne da  kisan gillar da HKI ta yi wa shugaban kungiyar Hamas, Isma’ila Haniyya a Tehran, shugaban kasar ta Iran ya bayyana cewa; Iran ce za ta ayyana lokacin daukar fansa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments