Shekaru 44 Da suka Gabata Amurka Ta Kasa Aiwatar Da Aikin Soje Don Kwato Amurkawa Da Suke Hannun JMI A Lokacin

A ranar 25 ga watan Afrilun shekara 1980 ne gwamnatin kasar Amurka na lokacin ta yi yunkurin farwa kasar Iran da yaki sannan ta kwato

A ranar 25 ga watan Afrilun shekara 1980 ne gwamnatin kasar Amurka na lokacin ta yi yunkurin farwa kasar Iran da yaki sannan ta kwato ma’aikatan ofishin jakadancinta kimani 50 da suke tsare a hannun JMI a lokacin.

Kafin haka dai a cikin watan Nuwamban shekara 1979 ne matasa yan jami’a masu bin tafarkin Imam Khomani (q) suka farawa ofishin jakadancin Amurka da ke nan Tehran inda suka kama ma’aikatanb ofishin jakadancin kimani 50 wadanda suke aikin liken asriwa wa gwamnatin Am,urka a kasar Iran da kuma yankin Asia ta kudu suka tsare.

Bayan kokarin kubutar da su ta hanyar Diblomasiyya ya ci tura, shugaba Cater ya yanke shawarar farwa kasar da yaki do kuma kwato wadannan Amurkawa. Don haka a rana irin ta yau suka shigo Iran ta gabacin kasar suka sauka a kusa da garin Tabas a kan wata tsohuwar tashar jiragen sama. Sannan daga nan suna son sui so Tehran da jitagen helkopta, amma sai aiki y abaci wasu jirage da sojojin Amurka suka kone a wurin wadanda suka saura kuma suke tsere suka bar kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments