Ministan harkokin wajen Iran ya gudanar da zaman tarurruka masu yawa da takwarorinsa a gefen zaman taron kolin kasashen musulmi na kungiyar hadin kan kasashen musulmi a birnin Banjul fadar mulkin kasar Gambiya
Ministan harkokin wajen kasar Iran Hussein Amir Abdul-Ilahiyon ya gana da takwararsa na kasar Sudan Hussein Awad tare da taya shi murnar nada shi a matsayin sabon ministan harkokin wajen Sudan gami da yi masa fatan samun nasara.
Ministan harkokin wajen na Iran ya jaddada rashin amincewar kasarsa da duk wani tsoma bakin kasashen waje a harkokin cikin gidan Sudan, yana mai fayyace shirin Iran na taimakawa wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar ta Sudan.
Sudan