Sudan Ta Mayar Da Martani Kan Ikrarin Chadi Na Rashin Taimakawa ‘Yan Tawayen Sudan

Ministan harkokin wajen Sudan Hussein Awad ya mayar da martani kan kalaman ministan harkokin wajen Chadi, inda ya musanta cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yan

Ministan harkokin wajen Sudan Hussein Awad ya mayar da martani kan kalaman ministan harkokin wajen Chadi, inda ya musanta cewa kasarsa tana goyon bayan ‘yan tawayen Sudan na dakarun kai daukin gaggawa. Yana mai jaddada cewa: Al’ummar Chadi tana da masaniyar yadda gwamnatin kasarta take tsoma baki a rikicin Sudan ta hanyar taimakawa ‘yan tawayen kasar.

Hussein Awad ya yi nuni da cewa, da dama daga cikin shugabannin siyasa, zamantakewa da na addini na kasar Chadi, suna yin Allah wadai da rawar da gwamnatin kasarsu take takawa a fagen taimakawa ‘yan tawayen Sudan musamman da makamai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments