Shugaban kungiyar Hizbullah Ta Kasar Lebanon Sheikh Na’im Qasim ya bayyana shahid Qasim Sulaimani shugaban rundunar Qudus ta JMI ya sami nasarar wargaza shirin Amurka a gabas ta tsakiya da kuma Afganisatan, wanda take son kungiyar ISIS ta aiwatar da shi.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto shahid Qasim yana fadar haka a jiya da yamma a wani jawabi na musamman da yayi don tunawa da Shihid Qasim sulaimani da kuma Mahadi Al-muhamndis wadanda shugaban kasar Amurka na lokacin ya bada umurnin kasheshi a ranar 3 ga watan Decemban shekara ta 2020.
Banda haka shahidan sun taimakawa Falasdinawa wajen ganin sun tsaya da kafafuwansu don fuskantar HKI. Ya ce Shahid kasim ya bawa falasdinawa horon soja da kuma duk abinda suke bukata don fuskantar HKI. Idan ba don shi da taimakon All..tun fako ba, da Falasdinawa ba zasu iya turjiya da jajircewar da suke yi a halin yanzu a gaza ba.
A wani bangaren na jawabinsa shugaban kungiyar ta Hizbullah ya ce kungiyarsa a shrye take tsab don sake komawa fagen fama da sojojin HKI, kafin karewar lokacin sulhu ko kuma bayan karewar amma a halin yanzu al-amura suna hannun gwamnatin kasar Lebanon don kula da irin yadda