Sheikh Na’im Kassim Ya Mika Sakon Ta’aziyyar Shahadar Gumari Na Kasar Yemen Ga Sayyid Husi

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya mika sakon ta’aziyyar shahadar babban hafsan hafsoshin sojan kasar Yemen Birgediya janar Muhammad Gumari ga shugaban Ansarullah

Babban sakataren kungiyar Hizbullah Sheikh Na’im Kassim ya mika sakon ta’aziyyar shahadar babban hafsan hafsoshin sojan kasar Yemen Birgediya janar Muhammad Gumari ga shugaban Ansarullah Sayyid Abdulmalik al-Husi.

Shekh Na’im Kassim ya bayyana alhininsa mai zurfi na rashin Shahid al-Gumari tare da bayyana shahada a matsayin wata daukaka bayan doguwar tafiya akan tafakin jihadi.Haka nan kuma ya bayyana cewa;shahidin na Yemen ya jagoranci sojojin kasar cikin jarunta, ya kuma taimaka wa Gaza wajen fuskanta laifukan ‘yan sahayoniya da Amurka.

Haka nan kuma babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya ce; yin shahadar jagorori wani alfahari da daukaka ne ga al’ummar musulmi, domin jinanensu sun hade a wuri daya, daga Yemen zuwa Lebanon da Iran da Iraki.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma taya sabon babban hafsan hafsoshin sojan kasar da aka zaba wanda ya maye gurbin shahidin janar Birgeriya Yusuf Hassan al-madani,murna.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai HKI ta kai hari a Yemen wanda ya yi sanadiyyar shahadar babban hafsan hafsoshin kasar janar Muhammd al-Gumari.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments