Sharhi : Kokarin Iran Na Ganin An Tsagaita Wuta A Game Da Abubuwan Dake Faruwa A Yankin

A ci gaba da ran gadin da yake a game da abubuwan dake faruwa a yankin Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya je kasar

A ci gaba da ran gadin da yake a game da abubuwan dake faruwa a yankin Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araghchi ya je kasar Siriya a kokarin ganin an tattauna da nufin samar da wani “shiri na tsagaita wuta a Lebanon da Gaza.

Bayan ziyararsa a Lebanon Abbas Araghchi ya je Syria, inda ya gana da takwaransa na Syria Al-Sabbagh.

Shugaban jami’an diflomasiyyar na Iran da yake zantawa da ‘yan jarida a filin jirgin sama na Damascus ya ce: Burina shi ne ci gaba da tuntubar diflomasiyya dangane da ci gaban da ake samu a yankin, na yi shawarwari masu matukar muhimmanci a birnin Beirut da jami’an gwamnatin Lebanon.

 Za mu ci gaba da tattaunawa da jami’an gwamnatin Siriya a Damascus don ci gaba da tuntubar juna.

A koyaushe muna tuntubar abokanmu na Siriya game da abubuwan da ke faruwa a yankin.

Tunda farko Ministan harkokin wajen kasar ta Iran Abbas Araqchi ya gana da shugaban gwamnatin rikon kwarya ta kasar Labanon Najib Mikati a ziyarar da ya kai birnin Beirut, ya kuma tabbatar da aniyar Tehran na goyon bayan kasar Labanon dangane da hare-haren da Isra’ila ke kai wa kasar.

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya jaddada cewa kasarsa ta kuduri aniyar tallafawa gwamnatin kasar Lebanon da al’ummarta da kuma tsayin daka wajen tunkarar ayyukan wuce gona da iri na Isra’ila.

Ministan na Iran ya ce; Tehran “za ta kaddamar da wani kamfen na diflomasiyya don tallafawa Lebanon,” inda ya bukaci taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi.

 Inda ya kara da cewa munanan laifukan da Isra’ila ta aikata kan Lebanon da Palasdinawa babban misali ne na laifukan yaki.

A daidai lokacin da ya isa ofishin jakadancin Iran da ke birnin Beirut, Araqchi ya jaddada wajabcin yin amfani da dukkan karfi da kuma karfin diflomasiyya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke da shi wajen tallafa wa kasar Labanon, wajen fuskantar munanan ayyukan da Kasar Isra’ila take aiwatarwa, tare da kiran kasashen musulmi da na Larabawa da su sauke nauyin da ya rataya a kansu dangane da hakan.

A nasa bangaren, Mikati ya nuna takaicinsa dangane da abin da ya bayyana a matsayin “rashin tasiri na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya wajen fuskantar bala’oi masu hatsarin gaske da yahudawan sahyoniya suke haddasawa a yankin gabas ta tsakiya.

A ci gaba da ran gadin da yake bayan ya isa kasar Siriya, Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi ya ce Tehran za ta ci gaba da bayar da cikakken goyon baya ga kasar Siriya da kuma fafutukar tsayin daka don tinkarar mamayar Isra’ila da halin da ake ciki a yankin.

Araghchi ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad a birnin Damascus a wannan Asabar

“Wannan matakin na Iran ya yi daidai da kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin da kuma tallafawa tsaron kasa na kasashen yankin,” in ji shi.

A nasa bangaren shugaban kasar Siriya ya yaba da matsayin Iran na goyon bayan al’ummar Palastinu da ake zalunta da kuma ‘yancin kare kai da kuma tsayin daka kan mamaya da wuce gona da iri na makiya yahudawan sahyoniya.

Assad ya ce dole ne kasashen duniya su yi kokarin kawo karshen bala’in da Isra’ila ke yi.

Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Siriya ya nakalto shugaban kasar yana cewa tsayin daka kan duk wani nau’i na mamaya da wuce gona da iri da kuma kisan jama’a hakki ne da ya dace.

Ya yaba da martini mai”karfi” da Iran ta mayar a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa kan kasashen yankin da keta hurumin kasashen yankin.

Ya kuma kara da cewa martanin da sojojin Iran suka yi a daren talata ya ba da darasi ga sahyoniyawan cewa turbar juriya tana da karfin dakile makiya, kuma za ta ci gaba da kasancewa mai karfi da tsayin daka saboda himma da hadin kan al’ummarta.

Shugaban na Syria ya kara da cewa Isra’ila ba ta da wani zabi illa ta dakatar da laifukan kisa da zubar da jinin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Ya kara da cewa Iran da Syria suna da alaka” waccce ke taka muhimmiyar rawa wajen tinkarar kalubale da hatsarin da yankin ke fuskanta, wanda mafi yawansu shi ne ci gaba da mamayar da Isra’ila ke yi a kasashen Larabawa da kuma kashe-kashen da gwamnatin kasar ke yi a kullum a kasashen Lebanon, Falasdinu da Syria.

Assad da Araghchi sun tattauna kan hanyoyin da za a bi wajen dakatar da hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon da kuma bukatar bayar da goyon baya ga kasar dangane da dubban ‘yan gudun hijira dake gudun hare-haren Isra’ila.

A wata ganawa da ya yi da ministan harkokin wajen Syria Bassam Sabbagh, Araghchi ya yi kira ga kasashen musulmi da na larabawa na yankin da su kara kaimi a fannin diflomasiyya da siyasa domin tilastawa magoya bayan Isra’ila dakatar da laifukan da take aikatawa.

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya yi tir da rashin daukar matakin kwamitin sulhu na MDD kan Isra’ila, sakamakon cikakken goyon bayan da Amurka da Birtaniya suke ba wa gwamnatin kasar da kuma kawo cikas ga matakin da kwamitin ya dauka na yanke shawarwarin da suka dace.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen kasar Syria ya jaddada muhimmancin kara hadin gwiwa tsakanin Tehran da Damascus a kungiyoyin duniya domin dakile keta dokokin kasa da kasa.

Manyan jami’an diflomasiyyar Iran da na Siriya sun tattauna kan yadda za a inganta dangantakarsu a bangarori daban-daban na siyasa da tattalin arziki da tsaro tare da yin kira da a aiwatar da dukkan yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka kulla a baya.

Araghchi da Sabbagh sun kuma yi musayar ra’ayi game da ci gaba da yakin kisan kiyashi da Isra’ila ke yi kan al’ummar Palastinu da kuma munanan hare-haren da take kaiwa Lebanon.

A wata ganawa da firaministan kasar Siriya Mohammad Ghazi Jalali, babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya ce Tehran ta kuduri aniyar inganta dangantakarta da Damascus a dukkan fannoni, musamman a fannin tattalin arziki.

A nasa bangaren, firaministan kasar Syria, ya yaba da goyon bayan Iran ga jajircewar da Falasdinu, da Lebanon da kuma Syria suka yi, wajen fuskantar hare-haren wuce gona da iri na Isra’ila.

Ya bayyana fatan cewa dukkan kasashen yankin za su fahimci cewa ci gaba da manufofin Isra’ila na da matukar barazana a gare su da kuma yin kokari matuka wajen dakile munanan ayyukan gwamnatin.

Har ila yau firaministan kasar Syria da ministan harkokin wajen kasar Iran sun tattauna kan aiwatar da yarjejeniyoyin da aka kulla tare da jaddada muhimmancin yin amfani da karfin sassa masu zaman kansu na kasashen biyu wajen bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki da masana’antu da kasuwanci.

Isra’ila ta kaddamar da yakin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoba bayan kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa ta kai wani harin ba-zata na ramuwar gayya kan zalun da ukuba da kumamar da take wa falasdinu.

Ya zuwa yanzu gwamnatin Isra’ila ta kashe akalla mutanen Gaza 41,825. Yayin da Wasu 96,910 kuma sun sami raunuka.

sanna Isra’ilar ta fara kai hari kan Lebanon tun watan Oktoban 2023, lokacin da ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza.

Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon tana mayar da martani ga wannan ta’addancin domin nuna goyan Falasdinawa.

Kungiyar ta sha alwashin ci gaba da kai hare-hare kan Isra’ila muddin gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da yakin Gaza.

Ya zuwa yanzu dai gwamnatin Isra’ila ta kauracewa duk wani kiraye-kirayen da kasashen duniya ke yi na tsagaita bude wuta tare da ci gaba da kai munanan hare-hare ta sama da kasa da kuma ta ruwa a zirin Gaza da gabar yammacin kogin Jordan da kuma Lebanon.

A ranar Talata, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta harba daruruwan makamai masu linzami zuwa ga sansanin sojojin Isra’ila, da kuma sansanonin leken asiri a duk yankunan da aka mamaye

Wannan farmakin ya zo ne a matsayin martani ga kisan gillar da gwamnatin kasar ta yi wa Ismail Haniyeh, shugaban ofishin siyasa na kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas, da babban sakataren kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sayyed Hassan Nasrallah, da kuma Birgediya Janar Abbas Nilforushan, mataimakin kwamandan ayyuka na Palasdinawa na Rundinar kare juyin juya halin Musulunci (IRGC).

A Yayin da yake gabatar da hudubar sallar Juma’a a birnin Tehran, Jagoran juyin juya halin Musulunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya yaba da irin gagarumin aikin da sojojin Iran suka yi wajen kaddamar da harin makami mai linzami a yankin Tel Aviv, yana mai cewa. Wanda ya ce ya dace kuma halaltacce ne”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments