Sayyid Husy: Sau Uku Muna Kai Wa Baban Jirgin Dakon Jiragen Yakin Amurka Na ” Eisenhower”

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husy wanda ya gabatar da jawabi a jiya Alhamis ya ce; Adadin jiragen ruwan da sojojin kasar

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik al-Husy wanda ya gabatar da jawabi a jiya Alhamis ya ce; Adadin jiragen ruwan da sojojin kasar su ka kai wa hari, sun kai 153, yayin da su ka kai hare-hare har sau uku akan babban jirgin ruwan dakon jiragen sama na yaki mai suna: Eisenhower”

Har ila yau Sayyid Abdulmalik al-Husy ya ce a cikin makon da ya shude kawai, sojojin Yemen din sun kai hare-hare har sau 10,inda su ka yi amfani da makamai masu linzamai masu cin dogon zango, jiragen sama marasa matuki, da kuma knanan jiragen ruwa har 26.

Wani sashe na jawabin Sayyid Abdulmalik al-Husy  ya kunshi cewa; Hatta a ranar babbar salla, sojojin kasar ta Yemen sun kai wasu hare-hare a cigaba da taimakawa masu jihadi a Gaza.

 Sai dai jagoran na kungiyar ta Ansarullah ya ce, hari mafi yin fice da su ka kai a cikin wannan makon, shi ne akan jirgin ruwa na dakon jiragen yakin Amurka ( Eisenhower) wanda shi ne karo na uku. Haka nan kuma nitsar da wani jirgin ruwan na Birtaniya mai suina: Totur, bayana da sojojin Yemen su ka kutsa cikin jirgin sannan su ka dasa abubuwa masu fashewa.

Sayyid Husy ya zargi Amurka da cigaba da ruruta wutar yaki da bai wa HKI kowane irin taimako na makamai da bama-bamai da jiragen yaki samfurin F15 domin cigaba da kashe al’ummar Falasdinu.

A halin da ake ciki a yanzu Amurkan tana shirin aikewa da wasu jiragen yaki 50 zuwa HKI.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments