Sayyid  Ali Sistani Ya Yi Kira Da A Kawo Karshen Harin Wuce Gona Da Iri Akan Kasar Lebanon

Babban marja’in addinin musulunci na kasar Iraki Sayyid Ali Sistani ya bayyana goyon bayansa ga al’ummar Lebanon da suke fuskantar hare-haren wuce gona da iri

Babban marja’in addinin musulunci na kasar Iraki Sayyid Ali Sistani ya bayyana goyon bayansa ga al’ummar Lebanon da suke fuskantar hare-haren wuce gona da iri ga HKI yake kai wa, tare da yin addu’ar akan Allah ya kare su daga masu nufinsu da sharri.”

Bugu da kari Ayatullah Sayyid Ali Sistani ya kuma yi addu’a ga Allah da ya yi wa wadanda su ka yi shahada rahama, ya kuma bai wa wadanda su ka jikkata lafiya.

Babban marja’in na addini ya kuma yi kira da a yi duk wani kokarin da za a yi yi domin ganin an kawo karshen wuce gona da iri na ‘yan sahayoniyar akan al’ummar Lebanon.

Wani sashe na bayanin Sayyid Sistani ya ambaci cewa; Al’ummar Lebanon mai daraja tana fuskantar matsanancin yayani a cikin kwanakin nan saboda hare-haren Isra’ila na wuce gona da iri.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments