Saudiyya Za Ta Yi Aiki Da Iran Saboda Karbar Bakuncin Kofin Duniya Na Kwallon Kafa A 2034

Jakadan kasar Saudiyya a Iran ya ce, kasarsa za ta yi aiki da Iran a lokacin da za ta karbi bakuncin wasannin kwallon kafa na

Jakadan kasar Saudiyya a Iran ya ce, kasarsa za ta yi aiki da Iran a lokacin da za ta karbi bakuncin wasannin kwallon kafa na duniya a shekarar 2034.

Jakadan na Saudiyya a Iran Abdullahi Bin Saud Al-anzi  ya bayyana hakan ne a yayin da ya gana da ministan wasanni da samari na Iran, Ahmad Donyamali a jiya Laraba.

Bangarorin biyu sun tattauna hanyoyin da za su aiki tare a lokacin da Saudiyyar za ta karbi bakuncin wasannin kwallon kafa na duniya.

Al-Anzi ya ce: “ Iran tana daga cikin kasashe mafi muhimmanci a wannan gasar wasannin da za a yi, kuma muna son bude tattaunawa a tsakanin manyan jami’an kasar akan yadda za mu yi aiki tare gabanin Saudiyyar ta karbi bakuncin wasannin kwallon kafa.”

A nashi gefen ministan wasannin na Iran ya jaddada cewa kasarsa tana cikin shirin yin aiki tare da Saudiyyar a cikin fagen wasanni da kuma cigaban matasa.

Haka nan kuma ministan ya yi ishara da yadda a shekara mai zuwa Saudiyya din za ta karbi bakuncin wasannan hadin kai na kasashen musulmi tare da cewa Iran din za ta halarta da tawaga mai karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments