Ma’aikatar makamashin kasar Saudiyya ta sanar da cewa, an kai wasu hare-hare masu yawa akan cibiyoyin makamashi da suke a kudancin kasar da hakan ya yi sanadiyyar tashin gobara a wasu cibiyoyin.
Sanarwar ma’aikatar makamashin ta Saudiyya ta ce da safiyar yau Talata ne aka kai wadannan munanan hare-haren da su ka dakatar da gudanar da ayyuka a cikin wasu daga cikinsu.
Dama dai tun da safiyar yau ne sojojin Yemen su ka ce ba da jimawa ba za su yi sanarwa akan wasu hare-hare da su ka kai a cikin kasar Saudiyya.
A jiya ne dai majalisar koli ta siyasar kasar Yemen ta yi tir da wasu hare-hare da Saudiyya ta kai a cikin kasar ta Yemen a gundumar Jauf, tana mai dorawa Saudiyya alhakin laifukan da aka tafka a sanadiyyar hare-haren.
Sanarwar ta kuma ce, abinda ya faru keta dokoki kasa da kasa ne, kuma tsokana ce mai hatsarin gaske.
A gefe daya, tun a jiya Talata ne dai sojojin Yemen su ka sanar da cewa sun harbo jiragen sama marasa matuki na Saudiyya guda 3 a cikin sa’o’I 24.
Rundunar sojan kasar Yemen ta sanar da kakkabo jirgin sama maras matuki na Saudiyya a karo na uku cikin sa’o’i 24 wanda ya rika shawagi a sararin samaniyar garin al-Baidha’a. Sanarwar da rundunar sojan na Yemen ta fitar ta kunshi cewa jiragen da ta harbo samfurin ” Wing Loong 11″ da aka yi amfani da makaman da su ka dace wajen kakkabo su.