Kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran ya fadawa HKI cewa; Na’urar kakkabo makamai masu lizamni ba za su iya kare ku ba, za mu yi galaba akanku.
Janar Husain Salami ya kuma kara da cewa, a halin da ake ciki a yanzu, makiya suna shirin kashe kansu da kansu ne, domin suna kan hanyar durkushewa.
Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musuluncin na Iran ya kuma ce; “yan sahayoniya su saurari sakamakon da zai same su, saboda munanan ayyukansu wanda shi ne zai shafe su daga doron kasa.”
Da yake Magana akan hari na biyu da Jamhuriyar musulunci ta kai wa HKI, wanda aka bai wa sunan: “Wa’adussadiq 2” janar Salami ya ce; “Yan sahayoniya suna kuskure, domin wa’adussadiq2’ ya tabbatar da cewa na’urorin tsaron da suke da su, ba su yi aiki ba, don haka na’urorin tsaro na thaad –wanda Amurka za ta ba su, ba zai yi aiki ba.
Har ila yau kwamandan dakarun kare juyin musulunci na Iran ya ce; Duk wani wuri da ku ka kai wa hari a Iran, to za mu kai hari a kwatankwacinsa da kuke da shi a cikin tsanani.”