Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran ya bayyana cewa: Akwai wani abu da ya haɗa Iran da Trump
Sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran, Dr Ali Larijani, ya tabbatar da cewa: Jamhuriyar Musulunci ta Iran ba ta adawa da manufar Shugaban Amurka Donald Trump na hana Iran mallakar makaman nukiliya.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al Jazeera, Dr Larijani ya bayyana cewa: Ka’idar rashin mallakar makaman nukiliya tana wakiltar wani tubali da za a gina a kai. Ya jaddada cewa: Shirin makamai masu linzami na Iran muhimmin bangare ne na tsaron kasarta kuma ba za a iya yin shawarwari a kai ba.
Dr Larijani ya sake nanata goyon bayan kasarsa ga tsarin tattaunawa mai adalci da ma’ana, yana mai cewa ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliya ta 2015 ya kawo cikas ga tsarin.