SADC : Zimbabwe Ta Karbi Ragamar Shugabancin Kungiyar Yankin

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya karbi ragamar jagorancin kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (SADC), na tsawon shekara guda a hukumance, yayin taron shekara-shekara da

Shugaban kasar Zimbabwe Emmerson Mnangagwa, ya karbi ragamar jagorancin kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (SADC), na tsawon shekara guda a hukumance, yayin taron shekara-shekara da ya gudana a birnin Harare.

Ya karbi shugabancin ne daga hannun takwaransa na Angola, Joao Laurenco a jiya Asabar, sannan kuma zai ba da sandar a shekara mai zuwa ga kasar Madagascar.

A cikin sanarwar hadin gwiwa, kasashe mambobin kungiyar sun yi marhabin da shiga tsakani da Angola ke jagoranta, na samun tsagaita wuta tsakanin Kinshasa, mamban ta SADC, da kuma Kigali.

Har ila yau, sun tabbatar da “goyon bayansu na ci gaba da karfafa zaman lafiya, tsaro da kwanciyar hankali.

Kasashe membobi kungiyar sun kuma yanke shawarar shirya taron gaggawa na ministocin kiwon lafiya na kasashensu don tantance illar kwayar cutar kyandar biri data bulla domin daukar mataki na bai daya.

Shugabannin sun kuma bukaci tallafin dala biliyan biyar don magance illolin mummunan fari a yankin.

Shugaban kungiyar mai barin gado, wanda kuma shi ne shugaban kasar Angola, Joao Laurenco, ya ce fiye da mutum miliyan 68 ne mummunan farin ya shafa a yankin a tsawon gomman shekaru.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments