Sabbin Hare-haren Isra’ila A Lebanon, Sun Kashe Mutum 37 Da Jikkata 150

Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce akalla mutane 37 ne suka mutu, sannan sama da 150 suka jikkata a harin da Isra’ila ta kai ranar

Ma’aikatar lafiya ta Lebanon ta ce akalla mutane 37 ne suka mutu, sannan sama da 150 suka jikkata a harin da Isra’ila ta kai ranar Alhamis, yayin da kasar ke ci gaba da kai hare-hare a kan Lebanon.

“Makiya sun kai hare-hare a cikin sa’o’i 24 da suka gabata … sun kashe mutane 37 tare da raunata 151,” in ji ma’aikatar lafiya a daren Alhamis.

Isra’ila ta kai hare-hare da dama a yankin Dahiyeh da ke kudancin Beirut a ranar Alhamis.

Gwamnatin ta yi amfani da bama-bamai masu karfi a cikin sabbin hare-haren ta, wadanda adadinsu ya haura goma sha biyu.

Gine-ginen farar hula da dama ne gwamnatin Isra’ilar ta kai wa hari.

Rahotanni sun nunar da cewa an yi amfani da karin bama-bamai a sabbin hare-haren idan aka kwatanta da harin da aka kashe shugaban kungiyar gwagwarmaya ta Hizbullah Sayyed Hassan Nasrallah a ranar Juma’ar da ta gabata.

Har ila yau, an kai hare-haren a kusa da filin jirgin sama na Beirut.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments