Rundunar Soja Ta “Khatamul Anbiya”: Babu Wani Tsaro  A Wannan Yankin Ba Tare Da Iran  Tana Da Shi Ba

Mataimakin kwamandan rudnunar soja ta “Khatamul-Anbiya” Kanar Miyomars Haydari,ya yi gargadi akan cewa; Duk wani hari da za a kawo wa kasar Iran, zai fuskanci

Mataimakin kwamandan rudnunar soja ta “Khatamul-Anbiya” Kanar Miyomars Haydari,ya yi gargadi akan cewa; Duk wani hari da za a kawo wa kasar Iran, zai fuskanci mayar da martani mai tsanani, sannan kuma ya kara da cewa; Babu yadda za a iya tabbatar da tsaro a cikin wannan yankin ba tare da Iran  tana da tsaron ba.

Haka nan kuma ya ce, taba tsaron Iran, yana nufin cewa babu wani wuri da zai zama mai aminci da zaman lafiya ga Amurka da kuma Isra’ila da kawayensu a cikin wannan yankin.

Dangane da yadda Amurka ta girke makamanta a cikin wannan yankin, mataimakin kwamandan rundunar ta ” Khatamul-Anbia” ya ce; babban kuskuren lissafi ne, idan kuwa har hakan ya ci gaba, to abinda zai sami Amurka shi ne shan kashi da zai tilasta mata ficewa daga yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted