Kakakin kwamitin tsaron kasa a majalisar shawarar musulunci ta Iran ya bayyana cewa; ” Ya zuwa yanzu ba za mu iya yin hukunci akan dalilan da su ka haddasa fashewar abubuwa a tashar ruwa ta Shahid Raja’i ba, amma za mu iya cewa babu hannu waje a ciki.
Kakakin kwamitin tsaron kasar ta Iran Ibrahim Rizai wanda ya halarci taron da aka yi a Majalisa akan fashewar da aka samu a tashar ruwan ta shahid Raja’i, ya kuma kara da cewa; Fahimtata da abinda na ji daga abokan aikina dangane da abinda ya faru a tashar ruwa ta Shahid Raja’i, da kuma rahotannin da su ka iso mana, shi ne cewa abinda ya farun ba shi da alaka da waje.”
A ranar Asabar da ta gabata ne dai wasu abubuwa su ka fashe a tashar ruwa ta Shahid Raja’i dake Bandar Abbas a kudancin Iran, wanda ya haddasa asarar rayuka da kuma jikkatar daruruwan mutane.
An bude kwamitin bincike domin gano hakikanin abinda ya faru a tashar da kuma haddas fashewar abubuwan masu karfi.