1
To yanzu Yemen ta shiga cikin yaki, Sahyuniyawa sun shiga fargabar cewa tattalin arzikinsu zai shiga matsala a mashigar Babul Mandab.
2
Ta yaya shigar Yemen cikin wannan yakin zai yi babban tasiri?
3
Na farko, karfin harba makamai masu linzami da jirage marasa matuka. Makamai masu linzami na rundunar sojin Yemen irin su Palastine 2, da jirage marasa matuka irin su Sammad 3 da makamantansu, wadanda suke cikin zangon fiye da kilo mita 2,000.
4
Wannan na nufin baya ga yankunan Falastinawa da aka mamaye, sauran sansanonin sojin Amurka a Tekun India, da Red Sea, da arewacin Afirka har ma da tekun Meditrenean, ba su a cikin aminci.
5
Na biyu, Mashigar Babul Mandab hanya ce ta gurgunta tattalin arzikin Isra’ila. Domin kuwa kashi 80 cikin dari na makamashin Isra’ila ana shigo da shi ne daga waje, kuma mafi yawa ta wannan mashiga.
6
A cikin shekara ta 2023 kawai, kimanin tan miliyan 100 na kayayyakin Isra’ila an shigo da su ne ta hanyar wannan mashiga. Yanzu da Yemen ta shiga wannan yaki, babu aminci ga Isra’ila a wannan mashiga.
7
Na uku, Gogewa a bangaren yaki ta kasa. Yemen kasa ce wadda take da gogewa ta fuskar irin wannan yaki, bayan yakin da Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa tare da taimakon Amurka suka kaddamar a kanta a shekarun baya.
8
Wannan kasa ta tabbatar da cewa tana da karfin kai hare-hare da kuma yaki ta kasa.
9
Shin ko Amurka da Isra’ila za su iya dakatar da Yemen?
10
Bayan harin 7 ga Oktoba, da kuma shigar Yemen domin taimakon Gaza, Amurka tare da kawancen kasashe fiye da 20 sun shiga yaki da Yemen.
11
Amma ya sakamakon ya kasance? Hare-Haren Amurka da Isra’ila da NATO ba su iya kawo karshen rufe mashigar Babul mandab da Yemen ta yi ba. Saboda haka shigar Yemen a cikin wannan yaki a halin yanzu, zai iya zama musabbabin gaggauta shan kayen Amurka da Isra’ila a wannan yaki.