Shan Kayen Trump

Wace rawa yaƙin Iran ya taka wajen shan kayen Trump da ’yan Republican? Bidiyon ya duba sakamakon zaɓe, tsadar rayuwa da makomar siyasar Amurka.

Share

Hoton haɗaka na Donald Trump, tutar Iran da ginin Majalisar Dokokin Amurka, mai taken Shan kayen Trump.

Iran ta yi sanadin samun sauyi a Mulkin Amurka! /// wannan kanun labari ne da wani shafin labarai na Amurka mai suna Newsweek, ya rawaito.

2

A zaben tsakiyar wa’adi, an yi wa Trump da ‘yan Republican mugun kaye.

3

‘Yan Democrat sun kwace Majalisun Dattawa da na Wakilai da rinjayen da ba a yi tsammani ba.

4

Kafafen yada labarai da dama sun rawaito cewa: Trump ya shiga yaki don canza gwamnati a Iran; amma sabanin haka Iran ce ta zame wa Trump da abokan kawancensa cikas.

5

A cewar wani bincike, kashi 63% na Amurkawa sun yi imanin cewa: harin da aka kai wa Iran kuskure ne.

6

Suna ganin cewa sakamakon wannan yaki ya sanya matsayin sojojin Amurka ya ruguje a duniya, haka zalika sansanonin Amurka da ke kewaye da Iran, sannan kuma lamarin ya shafi harkokin tattalin arziki da makamashi.

7

Mutane da yawa na cewa Isra’ila ta yaudari Amurka wajen ingiza ta har ta shiga yaki da Iran ba tare da wani dalili ba..

8

Mataimakin shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana a bainar jama’a cewa, yakin Amurka da Isra’ila a kan Iran shi ne babban dalilin shan kayensu a zaben, sannan ya yi kokarin nisanta kansa daga Trump.

9

Amma da wane irin salo ne Iran ta kayar da wata kasa mafi karfin tattalin arziki da na soja a duniya?

10

Masu sharhi a Amurka na cewa: Ba mu da cikakkiyar masaniya kan Iran, kuma kafofin watsa labaranmu sun yaudare mu.

11

A cewarsu, akidar gwagwarmaya da imani da Allah, shugabanci na gari, hadin kai tsakanin ‘yan kasa, da kuma manyan hazikan kwamandojin soja, duk basa daga cikin abin da ake fada a kafofin yada labarai. ///
Amma shin wannan ne karshen labarin? Ban yi tsammanin haka ba!

12

A cikin kwanakin nan Shugaban Iran ya gaya wa kwamandojin sojin kasar cewa, kada su yi tunanin iyakokin wata kasa wajen maida martani idan wani rikici ya sake barkewa.

13

Wannan yana nufin cewa duk wasu muradun abokan gaba na kasar har a wajen yankin suna cikin jerin abubuwan da zasu iya fuskantar harin martani.

14

A wata ma’anar kuma, barazanar soja ta Iran ga Amurka ta wuce yankin gabas ta tsakiya.

15

Yanzu dai dole ne mu jira domin ganin inda lamurran suka dosa, Domin ganin shin ko lokaci ya yi na kawo karshen babakere a kan al’ummomin duniya …