1
Ni da riba, Ku da asara!
2
Ta yaya Washington take dora dawainiyar yaki a kan kawayenta?
3
Salon siyasar wajen Amurka ya nuna cewa, Washington tana dora dawainiyar yaki a kan wasu kasashe, ita kuma ta kwashe ribar yakin.
4
Irin wannan ta faru sau da yawa. A yakin 2026 a kan Iran, gwamnatin Trump ta bukaci kasashen yankin Tekun Farisa da su biya biliyoyin daloli domin daukar nauyin yakin.
5
Amurka wadda ta kulla yarjejeniyar tabbatar da tsaro da wadannan kasashe, a yanzu ta jawo musu asara.
6
Irin wannan lamarin ya faru a lokacin yakin Tekun Farisa a shekara ta 1991, inda Amurka ce ta jagoranci yakin.
7
Amma kaso 88 cikin dari na dawainiyar yakin wato dala biliyan 54, Saudiyya, Kuwait, UAE, Jamus da Japan ne suka biya kudin, yayin da Amurka ta biya kaso 12 cikin dari ne kawai.
8
Haka nan bayan yakin duniya na biyu, kasashen da suka sha kaye kamar irin su Jamus da Japan, baya ga biyan tara, sun kuma rika biyan biliyoyin daloli a kowace shekara domin kula da sansanonin sojin Amurka a cikin kasashensu.
9
Wannan bai takaita da dora wa wasu dawainiya ba kawai, har ma da cin gajiya da kuma yin iko da kaddarorinsu.
10
A yakin Iraki a shekara ta 2003, kawancen Amurka, Burtaniya, Spain da kuma wasu kasashen NATO ne suka shiga yakin, amma bayan faduwar Saddam Hussain, an kafa Asusun Raya Kasar Iraki a karkashin kulawar Amurka, ta yadda dukkanin kudaden mai na Iraki za a rika zuba su ne a cikin Baitul Mali na Amurka.
11
Baya ga haka kuma, mafi yawan kwangilolin sake gina kasar Iraki an bayar da su ne ga kamfanonin Amurka, irin su HALLIBURTON da BECHTEL.
12
A batun yakin Ukraine ma da farko Amurka ta bayar da tallafi mai yawa, daga baya ta sanya sharadin kwasar ma’adanan Ukraine a madadin tallafinta, sannan ta dora wa kasashen Turai nauyin ci gaba da daukar dawainiyar yakin, tare da sayar musu da makamanta, inda a nan ma ta samu kazamar riba.
13
Abin da ke kunshe a cikin wannan salon dai a fili yake: kasashen da suka yi kawance da Amurka a cikin yaki su ne za su dauki nauyin dawainiyar yakin.
14
Amma sake gina kasar da aka yaka, ko sayar da makaman da ake yaki da su, duk wannan aikin Amurka ne kawai, wato ribar yakin za ta koma ga tattalin arzikin Amurka ne.
15
Yaki ba wai kawai fada ne na soja ba, ya zama wani salo ne na samun riba da habaka tattalin arziki, ta hanyar haifar da matsaloli da rashin tsaro ga wasu.