Bari mu dan yi tsokaci kan wasu bayanai game da Ingila a yau. Yayin da muke duba shafukan tarihi, muna ganin shafuka na zubar da jini da kisan mutane, laifin mutanen kawai shi ne sun kasance suna rayuwa a wuri mai arzikin albarkatun ƙasa da arzikin ɗan adam.