Ka taba jin cewa idan aka jefa kwado a cikin tafasasshen ruwa, zai yi tsalle ya fita, amma idan aka yi ta dumama ruwa a hankali a hankali, kwadon zai zauna a ciki har sai ya dahu.
A Yammacin Kogin Jordan, Isra’ila ba tare da sanarwar mamaya a hukumance ba, ta hanyar zartar da dokoki na gefe guda, ta canza rubutattun ka’idoji.
Majalisar Tsaron Isra’ila ta amince da wasu tsare-tsare da suka sake fasalin tsarin mamaya; matakin da mutane da yawa ke ganin cewa ya yi kama da salon hadiyar maciji.
Bisa yarjejeniyar Oslo, yankin A yana karkashin cikakken ikon Falasdinawa, yankin B gwamnatin farar hula ta Falasdinu da jami’an tsaron Isra’ila, yankin C kuma wanda shi ne kusan kashi 60% na Yammacin Kogin Jordan, zai kasance karkashin cikakken ikon Isra’ila.
Amma yanzu ikon zartarwa na Isra’ila ya kai har yankin A, bisa wasu dalilai kamar hana gine-gine marasa izini ko kare kayayyakin tarihi.