Shin Bom Ɗin Nukiliya Shi Ne Mafita?

An kai wa Iran hari ne ana tsakiyar tattaunawa akan batun Nukiliya,kuma abu mafi muhimmanci shi ne cewa an kai wannan harin ne akan ƙasar

Share

Shin bom ɗin nukiliya ne mafita, ko barazana ga duniya? Tarihi ya nuna cewa tsaro na gaskiya yana cikin adalci da dokoki, ba tsoro ba.

1
Shin duniya ta kai ga amincewa da cewa ƙera bom ɗin Nukiliya ne hanyar samun tsaro dawwamamme?

2
An kai wa Iran hari ne ana tsakiyar tattaunawa akan batun Nukiliya,kuma abu mafi muhimmanci shi ne cewa an kai wannan harin ne akan ƙasar da take memba acikin yarjejeniyar hana yaɗuwar makaman Nukiliya,kuma a hukumance ta sha nanata cewa shirin nata na zaman lafiya ba

3
Wannnan shi ne karo na biyu da aka zaɓi kai wa Iran hari ana kan ganiyar tattaunawar diplomasiyya. Abinda hakan yake nuna wa duniya shi ne cewa zama mamba a cikin ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa,ko yin wata yarjejeniya ta duniya ,ba za su bai wa wata ƙasa tsaro ba!
Menene dalili akan hakan ?
Abubuwan da su ka faru a tsawon tarihi su ne dalili.

4
Ƙasar Ukraniya ta miƙa dukkanin cibiyoyinta na Nukiliya a shekarun 1990’s, saboda ta sami tsaro.

5
Amma a ƙarshe aka kai ma ta hari.

6
Ƙasar Libya ta yi watsi da makamanta na Nukiliya,amma bayan wasu shekaru aka kifar da gwamnatin ƙasar.

7
Akasin waɗannan ƙasashen biyu, ƙasar Korea ta Arewa ta fice daga yarjejeniyar hana yaɗuwar Nukiliya a 2003,ta kuma ƙera makamin Nukiliya.

8
Daga lokacin da Korea ta Arewa ta ƙera makaman Nukiliya, babu wata ƙasa wacce ta ke yi ma ta barazanar kai ma ta hari,balle kuma ace an kai harin a kanta.

9
A wannan lokacin,bayan hare-hare biyu da aka kawo wa Iran ana tsakiyar tattaunawa,da kuma la’akari da abubuwan guda uku da su ka faru-da mu ka ambata- da akwai wani tunanin da yake yawo a duniya mai hatsari.

10
Wannnan tunanin shi ne cewa;Idan ba ka da makaman Nukiliya,To za a cutar da kai; wato abinda zai faru shi ne yaɗuwar makaman nukiliya da masana suke gargaɗi akansa.

11
A wannan lokacin da akwai ƙasashe 9 da suke da makaman nukiliya,a halin yanzu suke cikin tsaka mai wuyar; komawa kan aiki da diplomasiyya domin rage makaman Nukiliya,ko kuma shiga cikin wani sabon yanayi na gasar ƙera makaman nukiliya.
Amma Iran ta gabatarwa da duniya wata mafita ta uku;

12
Idan aka kammala wannan yaƙin da samun nasarar Iran,sannan kuma duniya ta goya ma ta baya akan biyanta asarar da aka jaza ma ta a yaƙi,haka nan kuma su yi tir da waɗanda su ka kawo wa Iran hari, a kuma ɗauke wa Iran takunkuman da aka ƙaƙaba ma ta.Abinda ya fi hakan muhimmanci shi ne yadda Iran za ta zama mai kula da Mashigar ruwan Hurmuz. Idan duk waɗannan abubuwan su ka faru,to sakamakon da zai faru shi ne tsarin takawa maƙiya birki ta hanyar kiyaye hurumin ƙasar da aiki da dokokin ƙasa da ƙasa,amma ba gasar ƙera makaman nukiliya ba.