Trump Da Wasan Rawar ‘Yan Mata Da Kasuwannin Kuɗi

Abinda Trump yake so shi ne a dakatar da duk wani sharhi akan abinda yake faruwa,maimakon hakan yana son mutane su riƙa jiran sanarwar da

Share

Hoton wani mutum mai kama da shugaban siyasa yana tsaye kusa da kasuwar kuɗi, tare da allon bayanai da ke nuna motsin kasuwa da jirgin mai a nesa

1
Abinda Trump yake so shi ne a dakatar da duk wani sharhi akan abinda yake faruwa,maimakon hakan yana son mutane su riƙa jiran sanarwar da za ta riƙa fitowa daga gare shi.

2
Dangane da rikicin da yake ,faruwa wanda yake da alaƙa da yaƙi akan Iran,da 0 wata halayya mai ban mamaki wacce take maimaita kanta.
A lokuta da dama Trump yana wallafa saƙwanni da yake sauya yanayin yaƙi da tattaunawa. Kwanaki kaɗan da su ka gabata ,acikin sa’a ɗaya kaɗai ,Trump ya wallafa saƙwanni 7. Ya bijiro da batutuwa guda 7 da dukkaninsu ba gaskiya ba ne.

3
Idan ya yi barazana,sai kuma ya juya zuwa batun tattaunawa. Daga nan kuma sai ya sauya zuwa amfani da harshe na kurari. Abinda yake yi ba wai yana a matsayin siyasa ba ne kaɗai:tamkar wata rawar ‘yan mata ce da yake yinta yana juyawa gaba,sannan ya kuma baya. A duk lokacin da ya yi hakan kuwa, sai kasuwannin su riƙa rausayawa tare da shi.

4
Trump ya sha tabbatar da cewa yana wallafa saƙwanninsa ne ba saboda ya isar da su ga mutane ba,yana amfani da su ne a matsayin makamin matsin lamba.
5
Trump ya yi wani abu wanda bai ba shi da tamka da shi ne,ya ambaci sunan kamfanin ‘Palantir Technologies” da ma’auninsa a kasuwar kuɗi:Wannan abinda ya yi ,ya yi kamar talla kai tsaye,ya yi tasiri kai tsaye a cikin kasuwar kuɗi da ƙarfafa ta.

6
Sai dai kuma ba a kowane lokaci ne kasuwa yake yin abinda yake so.saɓanin abinda aka tallata,hannun jari ya faɗi ƙasa. Kuma masu sharhi irin su Michael Burry ya bayyana cewa dama ƙimar da aka sanya ta jahar,ta wuce haddi.

7
Sai dai kuma da akwai wani yanayi da yake faruwa. A duk lokacin da aka ambaci sunan Iran da kuma yaƙin da ake yi,ƙimar man fetur tana ƙaruwa,idanu kuma suna komawa kan Mashigar ruwan Hurmuz; Mashigar ruwan ce wacce duk wani rikici a cikinta,kasuwar makamashi ta Duniya tana tangal-tangal.

8
Sai dai kuma idan ana kan ganiyar ruɗani,sai Trump ya sauya harshe yana cewa; ” tsagaita wuta”, “Abubuwa suna tafiya daidai”, “Babu buƙatar yaƙi”. Abinda zai biyo baya shi ne a sami natsuwa a kasuwa.
9
Abin tambaya anan shi ne:Shin Wannan wani nau’i ne na salon rage tasirin matsaloli?Ko kuma ƙoƙarin cin riba daga wani hargitsi da yake faruwa ?

10
Sakamakon da aka gani a ƙasa shi ne cewa saƙwanni irin waɗannan sun sauya ma’aunin hannun jari na S&p 500,ko kuma kasuwar man fetur ,a cikin mintuna kaɗan.

11
A cikin yanayi irin wannan, rahotanni suna bayyana cewa Trump yana wasa da kasuwanni. Amma kuma alokaci ɗaya abinda ya kamata ‘yan kasuwa da mutane su sani shi ne cewa wallafa saƙwanni ne a hanyoyin sadarwan na al’umma ne ake iya ba za su yaɓa maye gurbin nazari da bayani na masana da yake dogaro da abinda yake faruwa a ƙasa ba.

12
Kasuwannin da za su dogara da saƙwannin da ake tallafawa daga lokaci zuwa lokaci ,ba za su yi ƙarko ba.

13
Kamar yadda Muhammad Baƙir Ƙalibaf shugaban majalisar Iran ya ambata:Filin daga ne yake ayyana abinda zai faru ba shafukan sada zumunta ba.